Sai ƙasaitacciyar hargowa ta tashi, waɗansu malamai kuma na ɗariƙar Farisiyawa suka miƙe a tsaye, suka yi ta yin matsananciyar jayayya, suna cewa, “Mu ba mu ga laifin mutumin nan ba. In wani ruhu ne ko mala'ika ya yi masa magana fa?”