Littafi Mai Tsarki

A.m. 21:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da muka rabu da su da ƙyar, muka shiga jirgi muka miƙa sosai zuwa tsibirin Kos, kashegari kuma sai Rodusa, daga nan kuma sai Batara.

2. Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa ƙasar Finikiya, muka shiga muka tafi.

3. Da muka tsinkayo tsibirin Kubrus, muka mai da shi hagun, muka ci gaba zuwa ƙasar Suriya, muka sauka a Taya, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa.

4. Da muka sami inda masu bi suke, muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu ya iza su suka gaya wa Bulus kada ya je Urushalima.

5. Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.

6. Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.

7. Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da 'yan'uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.

8. Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.

9. Shi kuwa yana da 'ya'ya huɗu 'yan mata, masu yin annabci.

10. To, muna nan zaune 'yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.

11. Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ”