Littafi Mai Tsarki

Zab 13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Neman Taimako daga Wahala

1. Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji?Har abada ne?Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?

2. Har yaushe raina zai jure da shan wahala?Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana?Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?

3. Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini,Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.

4. Sa'an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba!Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba.

5. Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka,Zan yi murna gama za ka cece ni.

6. Zan raira waƙa ga Ubangiji,Gama ya kyautata mini.