1. Dukan jama'ar Isra'ila fa suka fito tun daga Dan a arewa har zuwa Biyer-sheba a kudu da kuma Gileyad daga gabas. Suka hallara gaba ɗaya a gaban Ubangiji a Mizfa.
2. Dukan shugabannin kabilar Isra'ila suna cikin wannan taron jama'ar Allah. Sojojin ƙafa yawansu ya kai dubu ɗari huɗu (400,000).