Littafi Mai Tsarki

Zab 98:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji,Gama ya aikata ayyuka masu banmamaki!Ta wurin ikonsa, da ƙarfinsa mai tsarki ya yi nasara.

2. Ubangiji ya bayyana cin nasararsa,Ya sanar da ikonsa na ceto ga sauran al'umma.

3. Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila,Da tabbatacciyar ƙauna da aminci.Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu!

4. Ku raira waƙa ta farin ciki ga Ubangiji.Dukanku waɗanda suke a duniya,Ku yabe shi da waƙoƙi, kuna ta da murya da ƙarfi,Saboda farin ciki!

5. Ku raira yabbai ga Ubangiji da garayu,Ku kaɗa garayu!

6. Ku busa kakaki da ƙahoni,Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, Sarki!

7. Ki yi ruri, ya ke teku,Ke da dukan masu rai waɗanda suke cikinki,Ki raira waƙa, ke duniya,Da dukan waɗanda suke zaune cikinki!

8. Ku yi tāfi, ya ku tekuna,Ku raira waƙa tare, ya ku tuddai, don farin ciki.

9. A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya!Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya.