Littafi Mai Tsarki

Zab 89:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Kai kake mulkin haukan teku,Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.

10. Ka ragargaza dodon nan Rahab, ka kashe shi,Da ƙarfin ikonka ka cinye maƙiyanka.

11. Duniya taka ce, haka ma samaniya taka ce,Kai ne ka halicci duniya da dukan abin da yake cikinta.

12. Kai ne ka yi kudu da arewa,Dutsen Tabor da Dutsen HarmonSuna raira waƙa gare ka don farin ciki.

13. Kai kake da iko!Kai kake da ƙarfi!

14. A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka,Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.

15. Masu farin ciki ne jama'ar da suke yi maka sujada, suna raira waƙoƙi,Waɗanda suke zaune a hasken alherinka.

16. Suna murna dukan yini saboda da kai,Suna kuwa yabonka saboda alherinka.