Littafi Mai Tsarki

Zab 89:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji zan raira waƙarMadawwamiyar ƙaunarka koyaushe,Zan yi shelar amincinka a dukan lokaci.

2. Na sani ƙaunarka za ta dawwama har abada,Amincinka kuma tabbatacce ne kamar sararin sama.

3. Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa,Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,

4. ‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki,Zan kiyaye mulkinka har abada.’ ”

5. Talikan da suke Sama suna raira waƙa a kanAbubuwan banmamakin da kake yi,Suna raira waƙa kan amincinka, ya Ubangiji.

6. Ba wani kamarka a Sama, ya Ubangiji,Ba wani daga su cikin talikai da yake daidai da kai.