Littafi Mai Tsarki

Zab 84:9-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Duba, ya Allah, kai ne garkuwarmu,Ka dubi fuskar Sarkinmu, zaɓaɓɓenka.

10. Kwana guda da za a yi a Haikalinka,Ya fi kwana dubu da za a yi a wani wuri dabam.Na gwammace in tsaya a ƙofar Haikalin Allahna,Da in zauna a gidajen mugaye.

11. Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja,Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja,Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

12. Masu farin ciki ne waɗanda suka dogara gare ka,Ya Allah Mai Runduna!