Littafi Mai Tsarki

Zab 84:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina ƙaunar Haikalinka ƙwarai,Ya Allah Mai Iko Dukka!

2. A can nake so in kasance!Ina marmarin farfajiyar Haikalin Ubangiji.Da farin ciki mai yawa zan raira waƙa ga Allah Mai Rai.

3. Har ba'u ma sukan yi sheƙa,Tsattsewa suna da sheƙunansu,A kusa da bagadanka suke kiwon 'ya'yansu.Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina, Allahna.

4. Masu murna ne waɗanda suke zaune a Haikalinka,Kullum suna raira yabonka!