Littafi Mai Tsarki

Zab 80:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka kasa kunne gare mu, ya Makiyayin Isra'ila,Ka ji mu, kai da kake shugaban garkenka,Da kake zaune a kan kursiyinka, a bisa kerubobi.

2. Ka bayyana ƙaunarka ga kabilar Ifraimu,Da ta Biliyaminu, da ta Manassa!Ka nuna mana ikonka,Ka zo ka cece mu!

3. Ka komo da mu, ya Allah!Ka nuna mana ƙaunarka, za mu kuwa cetu!