Littafi Mai Tsarki

Zab 74:8-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sun yi niyya su murƙushe mu sarai,Sun ƙone kowane tsattsarkan wuri na ƙasar.

9. Ba sauran tsarkakan alamu,Ba sauran annabawan da suka ragu,Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.

10. Ya Allah, har yaushe abokan gābanmu za su yi ta yi mana ba'a?Za su yi ta zargin sunanka har abada ne?

11. Me ya sa ka ƙi taimakonmu?Ka tasar musu ka hallaka su!

12. Amma ya Allah, kai ne Sarkinmu tun daga farko,Ka yi nasara da duniya.

13. Da ƙarfin ikonka ka raba teku,Ka farfashe kawunan dodannin ruwa,

14. Ka ragargaje kawunan kadduna,Ka kuwa ba mutanen hamada su ci.

15. Ka sa ruwan maɓuɓɓugai ya yi gudu,Ka sa manyan koguna su ƙafe.

16. Ka halicci yini da dare,Ka sa rana da wata a wurarensu.

17. Ka yi wa duniya kan iyaka,Ka kuwa yi lokatan damuna da na rani.

18. Amma ka tuna fa, ya Ubangiji, abokan gābanka suna yi maka ba'a,Su wawaye ne waɗanda suke raina ka.

19. Kada ka ba da jama'arka marasa taimakoA hannun mugayen maƙiyansu,Kada ka manta da jama'arka waɗanda ake tsananta musu!

20. Ka tuna da alkawarin da ka yi mana,Akwai tashin hankali a kowane lungu mai duhu na ƙasar!