Littafi Mai Tsarki

Zab 70:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka cece ni, ya Allah!Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!

2. Ka sa masu so su kashe ni,A ci nasara a kansu, su ruɗe!Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya!

3. Ka sa waɗanda suke mini ba'aSu razana sabili da fāɗuwarsu!

4. Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare kaSu yi murna, su yi farin ciki!Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonkaKullayaumi su ce, “Allah da girma yake!”

5. Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki,Ya Allah, ka zo wurina da hanzari.Kai ne mataimakina da Mai Cetona,Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji!