Littafi Mai Tsarki

Zab 60:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki,Edom kuwa kamar akwatin takalmina.Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”

9. Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?Wa zai kai ni Edom?

10. Da gaske ka yashe mu ke nan?Ba za ka yi tafiya tare da sojojinmu ba?

11. Ka taimake mu, mu yaƙi abokan gāba,Domin taimako irin na mutum banza ne!

12. Idan Allah yana wajenmu,Za mu yi nasara,Zai kori abokan gābanmu.