Littafi Mai Tsarki

Zab 6:4-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ya Ubangiji, ka zo ka cece ni,Gama kana ƙaunata, ka kuɓutar da ni daga mutuwa.

5. Ba za a tuna da kai a lahira ba,Ba wanda zai yabe ka a can!

6. Na gaji tiƙis saboda baƙin ciki,Kowane dare gadona yakan jiƙe saboda kukana.Matashin kaina ya yi sharkaf da hawaye.

7. Idanuna sun yi kumburi saboda yawan kuka,Har da ƙyar nake iya gani,Duk kuwa saboda abokan gābana!