Littafi Mai Tsarki

Zab 59:16-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Amma zan raira waƙa a kan ikonka,Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfiGa zancen madawwamiyar ƙaunarka.Kai mafaka ne a gare ni,Wurin ɓuya a kwanakin wahala.

17. Zan yabe ka, mai tsarona,Allah ne mafakata,Allah wanda ya ƙaunace ni.