Littafi Mai Tsarki

Zab 58:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Bari su ɓace kamar ruwan da ya tsanye,Bari a murtsuke su kamar ciyayi a hanya.

8. Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi,Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce.Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.

9. Kafin tukunya ta ji zafin wuta,Da zafin fushi, Allah zai watsar da su tun suna da rai.

10. Adalai za su yi murna sa'ad da suka ga an hukunta masu zunubi,Za su wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.

11. Mutane za su ce, “Hakika an sāka wa adalai,Hakika akwai Allah wanda yake shara'anta duniya!”