Littafi Mai Tsarki

Zab 57:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Daga sammai Allah zai amsa mini,Zai kori waɗanda suka tasar mini,Allah zai nuna mini madawwamiyar ƙaunarsa da amincinsa.

4. Raina yana tsakiyar zakoki,Na kwanta a tsakiyar waɗanda suka yi niyyar cinye mutane.Haƙoransu kamar māsu da kibau suke,Harsunansu masu kaifi ne kamar takobi.

5. Ka bayyana girmanka ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!

6. Maƙiyana sun kafa tarko don su kama ni,Damuwa ta fi ƙarfina.Sun yi wushefe a kan hanyata,Amma su da kansu suka fāɗa a ciki.

7. A shirye nake, ya Allah,Na shirya sosai!Zan raira waƙoƙi in yabe ka!

8. Ka farka, ya raina!Ku farka, molona da garayata!Zan sa rana ta farka!

9. Zan gode maka a cikin sauran al'umma, ya Ubangiji!Zan yabe ka a cikin jama'a!

10. Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai,Amincinka kuma har sararin sammai.

11. Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!