Littafi Mai Tsarki

Zab 56:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka yi mini jinƙai, ya Allah,Gama mutane sun tasar mini,Maƙiyana suna tsananta mini koyaushe!

2. Dukan yini maƙiyana suna tasar mini,Waɗanda suke faɗa da ni sun cika yawa.

3. Sa'ad da nake jin tsoro, ya Maɗaukaki,A gare ka nake dogara.

4. Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa,Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba.Me mutum kawai zai yi mini?

5. Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini,A kan kowane abu da nake yi,Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!

6. Sukan taru a ɓoye,Suna kallon duk abin da nake yi.Suna sa zuciya za su iya kashe ni.