Littafi Mai Tsarki

Zab 48:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Tsoro ya kama su suka razana,Kamar mace wadda take gab da haihuwa.

7. Allah yakan hallaka manyan jiragen ruwa da iskar gabas.

8. Mun ji labarin waɗannan al'amura,Yanzu kuwa mun gan suA birnin Allahnmu, Mai Runduna,Zai kiyaye birnin lafiya har abada.

9. A cikin Haikalinka, ya Allah,Muna tunanin madawwamiyar ƙaunarka.

10. A ko'ina jama'a suna yabonka,Sunanka ya game duniya duka.Kana mulki da adalci.

11. Bari jama'ar Sihiyona su yi murna!Gama kana shari'a ta gaskiya,Bari biranen Yahuza su yi farin ciki.

12. Ku tafi ku kewaye Dutsen Sihiyona,Ku ƙirga yawan hasumiyarsa.

13. Ku lura da garukanta, ku bincike kagaranta,Saboda ku iya faɗa wa tsara mai zuwa,

14. Cewa wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin,Shi ne zai bishe mu a dukan zamanai masu zuwa.