Littafi Mai Tsarki

Zab 48:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji mai girma ne,Dole kuwa a yabe shi da girmamawa a birnin Allahnmu,A kan tsattsarkan dutsensa.

2. Dutsen Sihiyona, dutse mai tsawo,Mai kyan gani ne na Allah,Birnin babban Sarki.Yakan kawo farin ciki ga dukan duniya!

3. Allah ya nuna akwai zaman lafiya a wurinsa,A kagarar birnin.

4. Sarakuna suka tattaru,Suka zo Dutsen Sihiyona,

5. Da suka gan shi sai suka yi mamaki,Suka tsorata suka gudu.