Littafi Mai Tsarki

Zab 44:19-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan,Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.

20. Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu,Muka yi addu'a ga gumaka,

21. Hakika ka gane,Domin ka san asirin tunanin mutane.

22. Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci,Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.

23. Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci?Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!

24. Me ya sa ka ɓuya mana?Kada ka manta da ƙuncinmu da wahalarmu!

25. Mun fāɗi, an turmushe mu a ƙasa,An bar mu kwance cikin ƙura.

26. Ka tashi ka taimake mu!Ka fanshe mu saboda madawwamiyar ƙaunarka!