Littafi Mai Tsarki

Zab 44:14-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Ka maishe mu abin raini a wurin arna,Suna kaɗa mana kai, suna raina mu.

15. Kullum a cikin kunya nake,Kunya ta lulluɓe ni ɗungum,

16. Saboda dukan wulakanci,Da zagin da nake sha daga maƙiyana da abokan gābana.

17. Dukan wannan ya same mu,Ko da yake ba mu manta da kai ba,Ba mu kuma ta da alkawarin da ka yi da mu ba.

18. Ba mu ci amanarka ba,Ba mu ƙi yin biyayya da umarnanka ba.

19. Duk da haka ka ƙi taimakonmu da namomin jejin nan,Ka bar mu a cikin duhu baƙi ƙirin.

20. Da a ce mun daina yin sujada ga Allahnmu,Muka yi addu'a ga gumaka,

21. Hakika ka gane,Domin ka san asirin tunanin mutane.

22. Ya Allah, saboda kai ne ake karkashe mu a kowane lokaci,Ake kuma maishe mu kamar tumakin da za a yanyanka.

23. Ka tashi, ya Ubangiji! Me ya sa kake zama kamar mai barci?Ka tashi! Kada ka yashe mu har abada!