Littafi Mai Tsarki

Zab 42:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Zurfafan tekuna suna kiran junansu,Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri!Igiyoyin ruwa na baƙin cikiSuka yi wa raina ambaliya.

8. Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana!Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare,In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.

9. Ga Allah wanda yake tsarona na ce,“Me ya sa ka manta da ni?Me ya sa nake ta shan wahalaSaboda muguntar maƙiyana?”

10. An ragargaza ni da zargin maƙiyanaWaɗanda suke tambayata kullum,“Ina Allahnka?”

11. Me ya sa ni ɓacin rai haka?Me ya sa ni damuwa?Zan dogara ga Allah.Har yanzu ma zan yabe shi,Mai Cetona, Allahna.