Littafi Mai Tsarki

Zab 40:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na yi ta jiran taimakon Ubangiji,Sa'an nan ya kasa kunne gare ni, ya ji kukana.

2. Ya fisshe ni daga rami mai hatsari!Ya aza ni a kan dutse lafiya lau.Ya kawar mini da tsoro.

3. Ya koya mini raira sabuwar waƙa,Waƙar yabon Allahnmu.Da yawa idan suka ga wannan za su tsorata,Za su kuwa dogara ga Ubangiji.

4. Mai farin ciki ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,Wanda bai juya ga gumaka ba,Ko ya haɗa kai da masu sujada ga allolin karya.

5. Ka yi mana abubuwa masu yawa, ya Ubangiji Allahna.Ba wani kamarka!Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka,Sun fi ƙarfin in faɗa.