Littafi Mai Tsarki

Zab 37:9-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Waɗanda suka dogara ga Ubangiji,Za su yi zamansu lafiya a ƙasar,Amma za a kori mugaye.

10. A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe,Za ka neme su, amma ba za a same su ba,

11. Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar,Su ji daɗin cikakkiyar salama.

12. Mugu yakan yi wa mutumin kirki makarƙashiya,Yana harararsa da ƙiyayya.

13. Ubangiji yana yi wa mugu dariya,Domin Ubangiji ya sani ba da daɗewa ba mugun zai hallaka.

14. Mugaye sun zare takuba,Sun tanƙware bakkunansuDon su kashe matalauta da masu bukata,Su karkashe mutanen kirki.

15. Amma takubansu za su sassoke su,Za a kakkarya bakkunansu.

16. Ƙanƙanen abin da mutumin kirki yake da shi,Ya fi dukan dukiyar mugaye amfani,

17. Gama Ubangiji zai raba mugaye da ƙarfinsu,Amma zai kiyaye mutanen kirki.

18. Ubangiji yana kula da masu yi masa biyayya,Ƙasar kuwa za ta zama tasu har abada.

19. Ba za su sha wahala a lokacin tsanani ba,Za su sami yalwa a lokacin yunwa.

20. Amma mugaye za su mutu,Magabtan Ubangiji kuwa za su shuɗe kamar furen jeji,Za su ɓace kamar hayaƙi.

21. Mugu yakan ci bashi, yă ƙi biya,Amma mutumin kirki mai alheri ne,Mai bayarwa hannu sake.

22. Waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka,Za su zauna lafiya lau a ƙasar,Amma waɗanda ya la'antaZa a kore su su fita.

23. Ubangiji yakan bi da mutum lafiyaA hanyar da ya kamata yă bi,Yakan ji daɗin halinsa,

24. In ya fāɗi, ba zai yi warwar ba,Gama Ubangiji zai taimake shiYă tashi tsaye.

25. Yanzu dai na tsufa, ni ba yaro ba ne,Amma ban taɓa ganin Ubangiji ya yar da mutumin kirki ba,Ko kuma a ga 'ya'yansa suna barar abinci.