Littafi Mai Tsarki

Zab 31:9-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji,Gama ina shan wahala,Idanuna sun gaji saboda yawan kuka,Na kuwa tafke ƙwarai!

10. Baƙin ciki ya gajerta kwanakina,Kuka kuma ya rage shekaruna.Na raunana saboda yawan wahalata,Har ƙasusuwana suna zozayewa!

11. Magabtana duka suna mini ba'a,Maƙwabtana sun raina ni,Waɗanda suka san ni kuwa suna jin tsorona,Sa'ad da suka gan ni a kan titi sukan guje mini.

12. Duk an manta da ni kamar matacce,Na zama kamar abin da aka jefar.

13. Na ji magabtana da yawa suna raɗa,Razana ta kewaye ni!Suna ƙulla maƙarƙashiya don su kashe ni.

14. Amma a gare ka na dogara, ya Ubangiji,Kai ne Allahna.

15. Kana lura da ni kullum,Ka cece ni daga magabtana,Daga waɗanda suke tsananta mini.

16. Ni, bawanka ne,Ka dube ni da alherinka,Ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka!

17. Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Kada ka bari a ci nasara a kaina!Ka sa a ci nasara a kan mugaye,Ka sa su yi shiru a lahira.

18. Ka rufe bakin maƙaryatan canDukan masu girmankai da masu fāriya,Waɗanda suke wa adalai maganar raini!

19. Abin al'ajabi ne irin tanadin da ka yi wa masu tsoronka!Abin da kake aikatawa a gaban kowa kuma,Yana da banmamaki.Kana kiyaye waɗanda suke amincewa da kai.

20. Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane,A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.

21. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Gama ya nuna mini ƙaunarsa mai ban al'ajabi,Sa'ad da aka kewaye ni, aka fāɗa mini!

22. Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka.Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.

23. Ku ƙaunaci Ubangiji, ku amintattun jama'arsa duka!Ubangiji yana kiyaye masu aminci,Amma yakan hukunta masu girmankai da tsanani.