Littafi Mai Tsarki

Zab 22:19-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji!Ka gaggauta ka cece ni, ya Mai Cetona!

20. Ka cece ni daga takobi,Ka ceci raina daga waɗannan karnuka.

21. Ka kuɓutar da ni daga waɗancan zakoki,Ba ni da mataimaki a gaban bijimai masu mugun hali.

22. Zan faɗa wa mutanena abin da ka yi,Zan yabe ka cikin taronsu.

23. “Ku yabe shi, ku bayin Ubangiji!Ku girmama shi, ku zuriyar Yakubu!Ku yi masa sujada, ku jama'ar Isra'ila!

24. Ba ya ƙyale matalauta,Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu,Ba ya rabuwa da su,Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”

25. Zan yabe ka a gaban babban taron jama'aSaboda abin da ka yi,A gaban dukan masu yi maka biyayya,Zan miƙa sadakokin da na alkawarta.

26. Matalauta za su ci yadda suke so,Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi,Su arzuta har abada!

27. Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji,Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya,Dukan kabilai za su yi masa sujada.

28. Ubangiji Sarki ne,Yana mulki a kan al'ummai.

29. Masu girmankai duka za su rusuna masa,'Yan adam duka za su rusuna masa,Dukan waɗanda aka ƙaddara musu mutuwa.