Littafi Mai Tsarki

Zab 19:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dubi yadda sararin sama yake bayyana ɗaukakar Allah!Dubi yadda suke bayyana a fili ayyukansa da ya yi!

2. Kowace rana tana shelar ɗaukakarsa ga ranar da take biye,Kowane dare yana nanata ɗaukakarsa ga daren da take biye.

3. Ba magana ko kalma da aka hurta,Ba wani amon da aka ji,

4. Duk da haka muryarsu ta game duniya duka,Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya.Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,

5. Tana fitowa kamar ango yana taƙama daga gidansa,Kamar ɗan wasan da ya ƙosa ya yi tsere.

6. Takan fara daga wannan ƙarshen sararin sama, ta kewaye zuwa wancan.Ba abin da zai iya ɓuya daga zafinta.

7. Dokar Ubangiji cikakkiya ce,Tana wartsakar da rai.Umarnan Ubangiji abin dogara ne,Sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita.