Littafi Mai Tsarki

Zab 18:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai duniya ta raurawa ta girgiza,Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgizaSaboda Allah ya husata!

8. Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.

9. Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,Tare da girgije mai duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa.

10. Ya sauko ta bisa bayan kerubobi,Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.

11. Ya rufe kansa da duhu,Gizagizai masu duhu cike da ruwa, suna kewaye da shi.