Littafi Mai Tsarki

Zab 18:5-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta,Kabari kuma ya ɗana mini tarko.

6. A shan wahalata na kira ga Ubangiji,Na yi kira ga Allahna domin neman taimako.A Haikalinsa ya ji muryata,Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

7. Sai duniya ta raurawa ta girgiza,Harsashin duwatsu suka jijjigu, suka girgizaSaboda Allah ya husata!

8. Hayaƙi ya yi ta tuƙaƙowa daga hancinsa,Harshen wuta da garwashi suna fitowa daga bakinsa.