Littafi Mai Tsarki

Zab 16:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allah, ka kiyaye ni, gama na zo gare ka neman mafaka.

2. Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Ubangijina,Dukan kyawawan abubuwan da nake da suDaga gare ka suke.”

3. Dubi irin martabar da amintattun jama'ar Ubangiji suke da ita!Ba abin da raina ya fi so,Sai in zauna tare da su.

4. Waɗanda suke hanzari zuwa ga gumaka,Za su jawo wa kansu wahala.Ba zan yi tarayya da su da hadayarsu ba.Ba zan yi sujada ga gumakansu ba.

5. Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji,Kai ne kake biyan dukan bukatata,Raina yana hannunka.