Littafi Mai Tsarki

Zab 147:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Abu mai kyau ne mu yabi Allahnmu,Abu mai daɗi ne, daidai ne kuma, a yabe shi.

2. Ubangiji yana rayar da Urushalima,Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.

3. Yakan warkar da masu karyayyiyar zuciya,Yakan ɗaure raunukansu.

4. Ya ƙididdige yawan taurari,Yakan kira kowanne da sunansa.

5. Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka,Saninsa ya fi gaban aunawa.

6. Yakan ɗaukaka masu tawali'u,Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.

7. Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,Ku yabi Allah da garaya.

8. Ya shimfiɗa gajimare a sararin al'arshi.Ya tanada wa duniya ruwan sama,Ya sa ciyayi su tsiro a kan tuddai.