Littafi Mai Tsarki

Zab 13:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji?Har abada ne?Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka?

2. Har yaushe raina zai jure da shan wahala?Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana?Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina?