Littafi Mai Tsarki

Zab 113:7-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Yakan ɗaga talakawa daga ƙura,Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.

8. Yakan sa su zama abokan sarakuna,Sarakunan jama'arsa.

9. Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta,Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!