Littafi Mai Tsarki

Zab 113:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Za a yabi sunansa yanzu da har abada!

3. Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji!

4. Ubangiji yake mulkin dukan sauran al'umma,Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai.

5. Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu.Yana zaune a can ƙwanƙolin sama,

6. Amma ya duba ƙasa,Ya dubi sammai da duniya.

7. Yakan ɗaga talakawa daga ƙura,Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.

8. Yakan sa su zama abokan sarakuna,Sarakunan jama'arsa.

9. Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta,Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!