Littafi Mai Tsarki

Zab 112:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Haske yakan haskaka wa mutanen kirki a cikin duhu,Da waɗanda suke yin alheri, da jinƙai, da gaskiya.

5. Mai farin ciki ne mutumin da yakan ba da rance hannu sake,Wato wanda yake yin harkarsa da gaskiya.

6. Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai,Ba za a taɓa mantawa da shi ba.

7. Ba ya tsoron jin mugun labari,Bangaskiyarsa tana da ƙarfi,Ga Ubangiji yake dogara.

8. Ba shi da damuwa ko tsoro,Ya tabbata zai ga faɗuwar maƙiyansa.

9. Yakan bayar ga matalauta hannu sake,Alherinsa kuwa dawwamamme ne.Zai zama mai iko wanda ake girmamawa.