Littafi Mai Tsarki

Zab 107:19-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. A cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga azabar da suke sha.

20. Da umarninsa ya warkar da su,Ya cece su daga kabari.

21. Dole su gode wa Ubangiji saboda madawwamiyar ƙaunarsa,Sabili da abubuwa masu banmamaki waɗanda ya aikata dominsu.

22. Dole su gode masa, su miƙa masa hadayu,Su raira waƙoƙin murna,Su faɗi dukan abin da ya yi!

23. Waɗansu suka yi tafiya a teku da jirage,Suna samun abin zaman garinsu daga tekuna.

24. Suka ga abin da Ubangiji ya aikata,Ayyukansa masu banmamaki waɗanda ya yi a tekuna.

25. Ya ba da umarni, sai babbar iska ta tashi,Ta fara hurowa, ta sa raƙuman ruwa su tashi.

26. Aka ɗaga jiragen ruwa sama,Sa'an nan suka tsinduma cikin zurfafa.Da mutanen suka ga irin hatsarin da suke ciki,Sai zuciyarsu ta karai.

27. Suka yi ta tuntuɓe suna ta tangaɗi kamar bugaggu,Gwanintarsu duka ta zama ta banza.

28. Cikin wahalarsu suka yi kira ga Ubangiji,Ya kuwa cece su daga azabarsu.

29. Ya sa hadiri ya yi tsit,Raƙuman ruwa kuma suka yi shiru.

30. Suka yi murna saboda wurin ya yi shiru,Ya kuma kai su kwatar jiragen ruwa lafiya,Wurin da suke so.