Littafi Mai Tsarki

Zab 106:45-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Saboda su ne ya tuna da alkawarinsa,Ya sāke ra'ayinsa saboda ƙaunarsa mai yawa.

46. Ubangiji ya sa waɗanda suka kama suSu ji tausayinsu.

47. Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu,Ka komo da mu daga cikin sauran al'umma,Domin mu yabi sunanka mai tsarki,Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.