Littafi Mai Tsarki

Zab 106:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Ubangiji!Ku yi wa Ubangiji godiya, gama nagari ne shi,Ƙaunarsa madawwamiya ce.

2. Wa zai iya faɗar dukan manya manyan ayyuka da ya yi?Wa zai iya yi masa isasshen yabo?

3. Masu farin ciki ne waɗanda suke biyayya da umarnansa,Waɗanda kullayaumi suke aikata abin da yake daidai!

4. Ka tuna da ni sa'ad da za ka taimaki jama'arka, ya Ubangiji!Ka sa ni cikinsu, sa'ad da za ka cece su.

5. Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka,In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu,In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.

6. Mun yi zunubi yadda kakanninmu suka yi,Mugaye ne, mun aikata mugunta.

7. Kakanninmu a MasarBa su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba,Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu,Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.

8. Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta,Domin ya nuna ikonsa mai girma.

9. Ya tsauta wa Bahar Maliya, ta ƙafe,Har ya bi da jama'arsa su hayeKamar a bisa busasshiyar ƙasa.

10. Ya cece su daga maƙiyansu,Ya ƙwato su daga wurin abokan gābansu.

11. Ruwa ya cinye maƙiyansu,Ba wanda ya tsira.

12. Sa'an nan jama'arsa suka gaskata alkawarinsa,Suka raira yabo gare shi.