Littafi Mai Tsarki

Zab 105:5-6-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5-6. Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.

7. Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.

8. Zai cika alkawarinsa har abada,Alkawaransa kuma don dubban zamanai,

9. Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim,Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.

10. Ubangiji ya yi madawwamin alkawari da Isra'ila,Ya yi madawwamiyar yarjejeniya da Yakubu sa'ad da ya ce,

11. “Zan ba ka ƙasar Kan'ana,Za ta zama mallakarka.”

12. Jama'ar Ubangiji kima ne,Baƙi ne kuwa a ƙasar.

13. Suka yi ta yawo daga ƙasa zuwa ƙasa,Daga wannan mulki zuwa wancan,

14. Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba,Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.

15. Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu,Kada ku cuci annabawana!”

16. Sa'ad da Ubangiji ya aukar da yunwa a ƙasarsu,Ya kuma sa abincinsu duka ya ƙare,

17. Sai ya aika da Yusufu ya riga su zuwa,Shi wanda aka sayar da shi kamar bawa.

18. Ƙafafunsa suka yi rauni saboda an ɗaure su da sarƙa,Aka kuma sa wa wuyansa ƙuƙumi na baƙin ƙarfe,

19. Har kafin faɗar da ya yi, ta cika.Maganar Ubangiji ta tabbatar da gaskiyar abin da ya faɗa.

20. Sa'an nan Sarkin Masar ya sake shi,Mai mulkin dukan sauran al'umma ya 'yantar da shi.

21. Ya sa shi ya lura da mulkinsa,Ya sa shi ya yi mulki a bisa dukan ƙasar.