Littafi Mai Tsarki

Zab 105:36-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Ya karkashe dukan 'ya'yan fari mazaNa dukan iyalan Masarawa.

37. Sa'an nan ya bi da Isra'ilawa, suka fita,Suka kwashi azurfa da zinariya,Dukansu kuma ƙarfafa ne lafiyayyu.

38. Masarawa suka yi murna da fitarsu,Gama sun tsoratar da su.

39. Ya sa girgije ya yi wa jama'arsa inuwa,Da dare kuma wuta ta haskaka musu.

40. Suka roƙa, sai aka ba su makware,Ya ba su abinci daga sama da za su ci su ƙoshi.

41. Ya buɗe dutse, sai ruwa ya bulbulo,Yana gudu cikin hamada kamar kogi.

42. Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkiWanda ya yi wa bawansa Ibrahim.

43. Haka kuwa ya bi da jama'arsa, suka fita suna raira waƙa,Ya bi da zaɓaɓɓun jama'arsa, suna sowa ta farin ciki.