Littafi Mai Tsarki

Zab 102:22-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Sa'ad da sauran al'umma da mulkoki suka taruDon su yi wa Ubangiji sujada.

23. Tun ina ƙaramin yaro Ubangiji ya sa na rasa ƙarfi,Ya gajerta kwanakina.

24. Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu,Tun da yake ban tsufa ba tukuna!Ya Ubangiji har abada kake.

25. Ka halicci duniya tun tuntuni,Da ikonka ne ka yi sammai.

26. Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama,Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa,Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.

27. Amma kai, kana yadda kake kullayaumin,Har abada kake.

28. 'Ya'yanmu za su yi zaman lafiya,Zuriyarsu kuma za su zauna cikin kiyayewarka kullayaumin.