Littafi Mai Tsarki

Zab 102:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada,Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.

13. Za ka tashi ka ji tausayin Sihiyona,Lokaci ya yi da za ka yi mata jinƙai,Wannan shi ne lokacin!

14. Bayinka suna ƙaunarta,Ko da yake an hallakar da ita,Suna jin tausayinta,Ko da yake ta zama kufai.

15. Sauran al'umma za su ji tsoron Ubangiji,Dukan sarakunan duniya za su ji tsoron ikonsa.

16. Sa'ad da Ubangiji ya sāke gina SihiyonaZai bayyana girmansa.

17. Zai saurari jama'arsa wadda ya rabu da ita,Zai kuwa ji addu'arta.

18. Ku rubuta abin da Ubangiji ya aikata don zamani mai zuwa,Don waɗanda ba a haife su ba tukuna,Su ma su yabe shi.

19. Ubangiji ya duba ƙasaDaga Sama, tsattsarkan wurinsa,Daga Sama ya dubi duniya,

20. Don ya ji nishin ɗaurarru,Don ya saki waɗanda aka yanke musu hukuncin kisa.

21. Saboda wannan mutane za su yi shelar sunan Ubangiji a Sihiyona,Za su yi masa godiya a Urushalima,

22. Sa'ad da sauran al'umma da mulkoki suka taruDon su yi wa Ubangiji sujada.

23. Tun ina ƙaramin yaro Ubangiji ya sa na rasa ƙarfi,Ya gajerta kwanakina.

24. Ya Allahna, kada ka ɗauke ni a yanzu,Tun da yake ban tsufa ba tukuna!Ya Ubangiji har abada kake.

25. Ka halicci duniya tun tuntuni,Da ikonka ne ka yi sammai.

26. Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama,Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa,Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.