Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.