Littafi Mai Tsarki

Mar 8:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A lokacin nan da wani taro mai yawan gaske ya sāke haɗuwa, ba su kuwa da abinci, sai ya kira almajiransa, ya ce musu,

2. “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna, ba su da wani abinci.

3. In kuwa na sallame su su tafi gida da yunwa haka, ai, za su kasa a hanya, ga shi kuwa, waɗansunsu sun fito nesa.”

4. Sai almajiransa suka amsa masa suka ce, “Ina za a iya samun gurasar da za ta ciyar da mutanen nan a jeji haka?”

5. Sai ya tambaye su, “Gurasa nawa gare ku?” Suka ce, “Bakwai.”

6. Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki gurasan nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiransa su kai wa taron, suka kuwa kakkai musu.

7. Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan. Da ya yi wa Allah godiya, sai ya ce su ma a kai musu.

8. Suka ci, suka ƙoshi, har suka ɗauki ragowar gutsattsarin, cike da manyan kwanduna bakwai.

9. Mutanen kuwa sun yi wajen dubu huɗu. Sai ya sallame su.

10. Nan da nan kuwa ya shiga jirgi da almajiransa, ya tafi ƙasar Dalmanuta.

11. Farisiyawa suka zo suka fara muhawara da shi, suna nema ya nuna musu wata alama daga sama, don su gwada shi.

12. Sai ya yi wata doguwar ajiyar zuciya, ya ce, “Don me mutanen zamanin nan suke neman ganin alama? Hakika, ina gaya muku, ba wata alamar da za a nuna wa mutanen wannan zamani.”

13. Daga nan ya bar su, ya sāke shiga jirgi, ya haye wancan ƙetaren.

14. Sun kuwa manta, ba su kawo gurasa ba, sai guda ɗaya ce kawai gare su a jirgin.

15. Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”