Littafi Mai Tsarki

Mar 6:19-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,

20. don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.

21. Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki.

22. Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Roƙe ni kome, sai in ba ki.”

23. Ya kuma rantse mata, ya ce, “Kome kika roƙe ni zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

24. Ta fita, ta ce wa uwa tata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.”

25. Nan da nan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa, ta roƙe shi, ta ce, “Ina so yanzu yanzu ka ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi.”

26. Sai sarki ya yi baƙin ciki gaya, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ba ya so ya hana ta.

27. Nan take sai sarki ya aiki dogari, ya yi umarni a kawo kan Yahaya. Ya tafi ya fille wa Yahaya kai a kurkuku,

28. ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa to ba uwa tata.

29. Da almajiran Yahaya suka ji labari, sai suka zo suka ɗauki gangar jikinsa, suka sa ta a kabari.

30. Manzannin suka komo wurin Yesu, suka faɗa masa duk iyakar abin da suka yi, da abin da suka koyar.

31. Ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita a wurin da ba kowa, ku ɗan huta.” Domin mutane da yawa suna kaiwa suna kawowa, ko damar cin abinci ma, manzannin ba su samu ba.