Littafi Mai Tsarki

Mar 15:23-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha.

24. Sa'an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri'a a kansu, su ga abin da kowa zai samu.

25. Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.

26. Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato “Sarkin Yahudawa.”

27. Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun. [

28. Wannan shi ne cikar Nassin nan da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.”]

29. Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! kai da za ka rushe Haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku,

30. to, sauko daga gicciyen, ka ceci kanka mana!”

31. Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura suka riƙa yi masa ba'a a junansu suna cewa, “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa,

32. Almasihun nan, Sarkin Isra'ila, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka gicciye tare da shi su ma suka zazzage shi.

33. Daidai rana tsaka, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

34. Da ƙarfe ukun sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāna?” wato “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”

35. Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, suka ce, “Kun ji yana kiran Iliya.”

36. Sai ɗayansu ya yiwo gudu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.”

37. Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, kana ya cika.

38. Sa'an nan labulen da yake cikin Haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa.

39. Sa'ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”