Littafi Mai Tsarki

Mar 15:21-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Sai ga wani mai wucewa, wai shi Saminu Bakurane, uban Iskandari da Rufas, yana zuwa daga ƙauye. Suka fa tilasta masa ya ɗauki gicciyen Yesu.

22. Suka kai Yesu wani wuri wai shi Golgota, wato wurin ƙoƙon kai.

23. Suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, amma ya ƙi sha.

24. Sa'an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri'a a kansu, su ga abin da kowa zai samu.

25. Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.

26. Aka kuma rubuta sanarwar laifinsa sama da shi, wato “Sarkin Yahudawa.”

27. Suka kuma gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya dama da shi, ɗaya kuma a hagun. [

28. Wannan shi ne cikar Nassin nan da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.”]

29. Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai, suna cewa, “Ahaf! kai da za ka rushe Haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku,

30. to, sauko daga gicciyen, ka ceci kanka mana!”

31. Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura suka riƙa yi masa ba'a a junansu suna cewa, “Ya ceci waɗansu, ya kuwa kasa ceton kansa,

32. Almasihun nan, Sarkin Isra'ila, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka gicciye tare da shi su ma suka zazzage shi.

33. Daidai rana tsaka, sai duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.

34. Da ƙarfe ukun sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāna?” wato “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”

35. Da waɗansu na tsaitsayen suka ji haka, suka ce, “Kun ji yana kiran Iliya.”

36. Sai ɗayansu ya yiwo gudu, ya jiƙo wani soso da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha, yana cewa, “Bari mu gani ko Iliya zai zo ya sauko da shi.”