Littafi Mai Tsarki

M. Had 3:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Dukan abin da ya faru, ya riga ya faru a dā. Allah ya sa abin da ya faru ya yi ta faruwa. Allah yana hukunta abin da ya riga ya faru.

16. Banda wannan kuma, na gane a duniyar nan mugunta ta gāje matsayin adalci da na abin da yake daidai.

17. Sai na ce a zuciyata, “Da adali, da mugu, Allah zai shara'anta su, domin an ƙayyade lokaci na yin kowane abu da na yin kowane aiki.”

18. Na dai ce Allah yana jarraba mutum ne domin ya nuna masa bai ɗara dabba ba.

19. Gama makomar 'yan adam da ta dabbobi ɗaya ce, yadda ɗayan yake mutuwa haka ma ɗayan. Dukansu numfashinsu iri ɗaya ne. Mutum bai fi dabba ba, gama rai ba shi da wata ma'ana ga kowannensu.

20. Dukansu wuri ɗaya za su tafi, gama dukansu biyu daga turɓaya suka fito, dukansu biyu kuma za su koma cikinta.

21. Wa zai iya tabbatarwa, cewa ruhun mutum zai tafi sama, ruhun dabba kuwa zai tafi ƙasa?