Littafi Mai Tsarki

M. Had 3:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Dukanmu mu ci, mu sha, mu yi murna da abin da muka yi aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.

14. Na sani dukan abin da Allah ya yi zai dawwama, ba abin da za a ƙara, ko a rage. Allah ya yi haka kuwa domin mutane su zama masu tsoronsa.

15. Dukan abin da ya faru, ya riga ya faru a dā. Allah ya sa abin da ya faru ya yi ta faruwa. Allah yana hukunta abin da ya riga ya faru.

16. Banda wannan kuma, na gane a duniyar nan mugunta ta gāje matsayin adalci da na abin da yake daidai.

17. Sai na ce a zuciyata, “Da adali, da mugu, Allah zai shara'anta su, domin an ƙayyade lokaci na yin kowane abu da na yin kowane aiki.”

18. Na dai ce Allah yana jarraba mutum ne domin ya nuna masa bai ɗara dabba ba.